Wasu matasa sun kona gine-ginen gwamnati da na 'yan Shi'a a Iraki

Wasu matasa da suka fusata a garin Basra na Iraki sun kona gidan talabijin din gwamnati da kuma wasu gine-ginen 'yan Shi'a.

Wasu matasa sun kona gine-ginen gwamnati da na 'yan Shi'a a Iraki
Bidiyon yadda al'amuran suka kicime a garin Basra na Iraki
Bidiyon yadda al'amuran suka kicime a garin Basra na Iraki

Bidiyon yadda al'amuran suka kicime a garin Basra na Iraki

Wasu matasa da suka fusata a garin Basra na Iraki sun kona gidan talabijin din gwamnati da kuma wasu gine-ginen 'yan Shi'a.

Masu zanga-zangar adawa da rashin aikin yi da cin hanci da ya dabi kasar, sun shiga gidan talabijin din garin da kuma ginin kungiyar Badir. Sun kona gine-ginen tare da kona wata motar yada shiri kai tsaye.

Wasu masu zanga-zangar kuma sun koma ginin wata kungiya da aka ce ta magoya bayan Iran ce karkashin jagorancin Ammar Al-Hakim.

Haka zalika sun kona ginin jam'iyyar Firaministan Iraki Haidar Al-Abadi.

An yada hotuna da bidiyon yadda aka kona gi,ine-ginen.Labarai masu alaka