Gwaggon biri mafi tsufa a duniya ya mutu yana da shekaru 62

Gwaggon biri mafi tsufa a duniya mai shekaru 62 da haihuwa ya mutu a gidan ajje namun daji na Perth da ke Kasar Ostireliya.

Gwaggon biri mafi tsufa a duniya ya mutu yana da shekaru 62

Gwaggon biri mafi tsufa a duniya mai shekaru 62 da haihuwa ya mutu a gidan ajje namun daji na Perth da ke Kasar Ostireliya.

Tun shekarar 1968 gwaggon birin ya ke gidan ajje namun dajin na Perth kuma akwanakin baya saboda tsufa ya sanya aka yi masa allurar barci.

Gwaggon birin mai suna Puan yana da 'ya'ya 11 da jikoki 54 kuma ana kiran sa sunan tsohon dattijo a gidan gonar.

A shekarar 2016 ne aka bayyana birin a matsayin mafi tsufa a duniya inda ya shiga littafin tarihi na "Guinness Book of Record."

Hukumar Kare Namun Daji ta Duniya  ta ce, akwai gwaggon birin nau'in Sumatra dubu 14,600 a duniya baki daya.Labarai masu alaka