Firaministan Faransa ya halarci taron bude baki a Paris

Firaministan Faransa Edouard Philippe, ministan harkokin cikin gida Gerard Collomb da kuma wasu manyan yan siyasar kasar hadi da kungiyoyin addini sun gana a yayın bude baki da gwamnatin kasar ta shirya.

Kungiyoyin addinin lslam da dama hađi da kungiyar haddin kan Musulmi a Faransa sun halarci bude bakin. 

Baya ga shugaban haddin kan Musulmi a kasar Ahmet Ogras jakadan Turkiyya a Faransa lsmail Hakki Musa da kuma jakadan Saudiyya a Paris.

Bayan kamala bude bakin firaministan Faransa Edouard Philippe ya godewa shugabannin addinan saboda gayyatarsa da aka yi.

Ministan harkokin cikin gidan Faransa kuwa ya yi kira akan daukan matakan da suka dace domin warware matsalolin addini a kasar. 

Shugaban kungiyar haddin kan Musulmi a Faransa ya bayyana cewar kungiyar na iya kokarin ta wajen kawo sauyi akan harkokin addini a kasar. Labarai masu alaka