An gudanar da tattatakin ranar Kudus a Landan

Wata Kungiyar Kare Hakkokin Musulmai da ke Landan Babban Birnin Kasar Birtaniya tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyin farar hula sun gudanar da tattakin "Ranar Kudus".

Kusan mutane dubu 10 ne suka halarci tattakin.

 An fara tattakin daga bakin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Landan inda mutanen suka daga allunan sukar manufofin Isra'ila, Amurka, Ingila da Saudiyya kan kasar Falasdinu.

Rahotanni sun ce, wasu magoya bayan Isra'ila kusan su 30 ma sun taru a wajen.

Mutanen da suka  nuna goyon baya da Shugaban Amurka Donald Trump tare da wasu masu tsaurin ra'ayi sun dinga zagi da kai hari kan masu adawa da Kasashen na Yamma da ke zaluntar Falasdinawa.

Ingilawan masu tsaurin ra'ayi sun rera taken goyon baya ga Mai Kyamar Islama Tommy Robinson da aka yanke wa daurin watanni 13 a gidan yari.

An kama wasu daga cikin masu tsaurin ra'ayin bayan sun fafata artabu da 'yan sanda.Labarai masu alaka