An haramtawa 'yan makaranta amfani da wayar hannu a Faransa

Majalisar Dokkin kasar Faransa ta amince da dokar hana 'yan makarantar firamare da na kusa da sakandare amfani da wayar hannu.

An haramtawa 'yan makaranta amfani da wayar hannu a Faransa

Majalisar Dokkin kasar Faransa ta amince da dokar hana 'yan makarantar firamare da na kusa da sakandare amfani da wayar hannu.

A yayin kada kuri'a akan dokar mafi yawan 'yan majalisun sun daga hannu dake nufin amincewarsu akan saka dokar da za ta haramtawa 'yan makaranytar firamare da na kusa da sakandare amfani da wayar hannu.

A dokar da za ta fara amfani a watan Satumba bayan an bude makarantu, ana kokarin yi mata kwaskwarima domin a cire dokr akan malaman makarantu.

A karshen shekarar 2017 ministan ilimin kasar Jean-Michel Blanquer, ya fitar da wata sanarwa inda ya ce za'a haramtawa dalibai amfani da wayar hannu domin su natsu akan darusukan su.

Dokar dai kawo yanzu bata shafi manyan 'yan makarantar sadandare ba.

 Labarai masu alaka