Paparoma: Danganta Musulunci da ta'addanci jahilci ne

Jagoran ruhaniya ta cocin Katolika Paparoma Franciscus ya bayyana cewar danganta Musulunci da ta'addanci kuskure ne kuma abin ki.

Paparoma: Danganta Musulunci da ta'addanci jahilci ne

Jagoran ruhaniya ta cocin Katolika Paparoma Franciscus ya bayyana cewar danganta Musulunci da ta'addanci kuskure ne kuma abin ki.

Kamar yadda kanfanin dillancin labaran ANSA na Antaliya ya rawaito a jawabin da jaridar "L'Eco di Bergamo" ya buga Paparoman ya bayyana cewar akwai muhinmanci ga addinai su hada kai, lamarin da suke taka rawar gani a kai.

A yayinda Paparoma ke jawabi akan yadda wasu da'ira ke danganta Musulunci da ta'addanci ya bayyana cewar:

"Shin kuna ganin ya kamata a danganta Musulunci da ta'addanci? Wadansu mutane suna yin hakan amma wannan kuskurene, karyace kuma jahilci"

Paparoma Franciscus ya kara da cewa ko a cikin majami'un kiristanci za'a iya yin amfani da "karfin yaki" domin samun mulki duk da hakan ba domin "lumana ba sai dai domin burin kungiya."

 Labarai masu alaka