An kama bakin haure 37 a Turkiyya

A yankin lardin Van na Turkiyya an kama bakin haure 37 da suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba.

An kama bakin haure 37 a Turkiyya

A yankin lardin Van na Turkiyya an kama bakin haure 37 da suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba.

Sanarwar da Helkwatar Jandarma ta lardin ta fitar ta ce, jami'ansu na gundumar Tushba ne suka kama mutanen a kauyen Salamtash a lokacin da suke cikin motar bas.

An kama mutanen su 37 da suka fito daga Afganistan wanda sun shiga Turkiyya ta barauniyar hanya.

An kama direban motar inda ake kuma ci gaba da bincike kan mutanen.

 Labarai masu alaka