Shugaban Kasar Koriya ta Arewa ya haramta duk wani taro na shan giya ko rawa da kida

Shugaban Kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya haramta duk wasu taruka da za a dinga shan giya/barasa kokuma yin raye-raye.

An bayyana cewa, babbar manufar wannan mataki shi ne magance matsalar takunkumin tattalin arzikin da aka saka wa kasar.

Duk da korafin kasashen duniya amma Koriya ta Arewa ba ta daina gwada harba makamai masu linzami ba wanda hakan ya sa aka saka mata takunkuman tattalin arziki.

Hukumar Leken Asiri ta Koriya Kudu ta ce, gwamnatin Pyongyang ta hana duk wasu taruka da za a dinga rawa da kida ko shan giya, inda ta kuma sake tsaurara matakan tsaro kan duk wani bau da ba ta masaniya a kai.

Al'umar Koriya ta Arewa dai na ci gaba da rayuwa a cikin halin kuncin rayuwa.Labarai masu alaka