Za a bude babban dakin karatu da Turkiyya ta samar a Afirka ta Kudu

Wata cibiyar raya al'adu ta Turkiyya za ta kaddamar da babban dakin karatu da ta gina a kasar Afirka ta Kudu a wata mai zuwa.

Za a bude babban dakin karatu da Turkiyya ta samar a Afirka ta Kudu

Wata cibiyar raya al'adu ta Turkiyya za ta kaddamar da babban dakin karatu da ta gina a kasar Afirka ta Kudu a wata mai zuwa.

Shugaban Cibiyar ta Yunus Emre Gokhan Kahraman ya ce, sun kafa dakin karatun ne don amfanin masu binciken Afirka ta Kudu da na Turkiyya.

Ya ce, an saka wa dakin karatun suna ABubakar Efendi.

Efendi shi ne mutumin da DaularUsmaniyya a lokacin Sarki Abdulaziz ta tura zuwa Afirka ta Kudu don bayar da ilimi ga Musulman Cape Twon a shekarar 1863.

Kahraman ya ce, Efendi ne ya fara kafa cibiyar ilimi a Cape Town.Labarai masu alaka