Mutane 7 sun mutu sakamakon fashewar tankar mai a Najeriya

Mutane 7 ne suka rasa rayukansu sakamakon fashewar wata tankar mai a jihar Anambra dake kudu maso-gabashin Najeriya.

Mutane 7 sun mutu sakamakon fashewar tankar mai a Najeriya

Mutane 7 ne suka rasa rayukansu sakamakon fashewar wata tankar mai a jihar Anambra dake kudu maso-gabashin Najeriya.

Kakakin 'yan sandan jihar Anambra Haruna Muhammad ya bayyana cewa, a garin Awka na jihar ne fashewar da ba a san me ya janyo ba ta afku.

Muhammad ya kara da cewa, akwai karin mutane da damas da suka jikkata sakamakon fashewar.

Ya ce, an kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti inda  aka kuma fara bincike game da hatsarin.Labarai masu alaka