An sanar da dokar ta baci a wasu yankunan Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta sanar da dokar ta baci game da cutar zazzabin Lassa da ake dauka daga dabbobi wanda ke kashe mutane.

An sanar da dokar ta baci a wasu yankunan Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta sanar da dokar ta baci game da cutar zazzabin Lassa da ake dauka daga dabbobi wanda ke kashe mutane.

Daraktan Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya Chikwe Ihekweazu ya sanar da cewa, sakamakon yawaitar bullar zazzabin Lassa sun sanar da dokar ta baci inda aka fara aiyuka na musamman don yaki da cutar.

A shekarar da ta gabata a jihohi 23 na Najeriya mutane dubu 3 da 229 ne cutar zazzabin Lassa ta kama wadanda 146 suka rasa rayukansu.

Ya ce, daga farkon watan Janairu zuwa yau mutane 60 sun kamu da cutar a jihohin Najeriya 8.

Iheakweazu ya fadi cewa, cutar za ta ci gaba da yaduwa har nan da watan Afrilu inda ya kuma gargadi jama’a da su kula da tsafta sannan su nisanci beraye da dabbobi makamantansu.

Cutar Lassa da ake dauka daga kashin bera na harbuwa zuwa mutum daga mutum inda tana kuma kisa.Labarai masu alaka