Kwarankwatsa ta fado wa wasu masu wasan kwallon kafa a Burundi

Mutane 4 ne suka mutu sakamakon fadowar kwarnkwatsa a filin wasan kwallon kafa a lokacinda ake tsaka da buga wasa.

Kwarankwatsa ta fado wa wasu masu wasan kwallon kafa a Burundi

Mutane 4 ne suka mutu sakamakon fadowar kwarnkwatsa a filin wasan kwallon kafa a lokacinda ake tsaka da buga wasa.

Labaran da jaridun Burundi suka fitar na cewa, kwarankwatsa ta fada a tsakiyar filin wasan kwallo a garin Ngozi dake da nisan kilomita 120 daga Bujumbura Babban Birnin Kasar kuma mafi yawan jama’a.

Kwarankwatsar ta fado wa ‘yan wasa 6. Biyu daga cikinsu sun mutu nan take, biyu kuma sun mutu bayan an kai su asibiti. Ana ci gaba da kula da lafiyar ‘yan wasa 2 da suka jikkata.

A kowacce shekara ana samun Ibtila’i a Burundi sakamakon mamakon ruwan sama da guguwa da ake fuskanta.

Ma’aikatar Kula da Harkokin Zamantakewa ta fitar da alkaluman cewa a shekarar da ta gabata Ibtila’oin sun shafi iyalai dubu 60.Labarai masu alaka