"To sai me in Saudia ta kashe Kashoggi ?"

Shugban kasar Comoros,Azali Asumani ya ce, yana mamakin yadda duniya ke ci gaba da sukar lamairin Masarautar Saudia saboda ta kashe dan jarida Jamal Kashoggi.

"To sai me in Saudia ta kashe Kashoggi ?"

Shugban kasar Comoros,Azali Asumani ya ce, yana mamakin yadda duniya ke ci gaba da sukar lamairin Masarautar Saudia saboda ta kashe dan jarida Jamal Kashoggi.

Abinda yasa tuni mutane daga ciki da wajen kasar Comoros suka yi caa kan Asumani,wanda suke ganin cewa ya fita zakka a sahun shugabannin duniya wadanda ke fafutukar tabbatar da doka da oda.

Shugaban na Tsibiran Comoros dai cewa yayi: "Shin ina laifi,don an kashe dan Saudia a ofishin jakadanci kasarsa?" Bukatata ita ce, an sanar da Sarki Salman cewa babu abin tashin hankali a nan.A kowace safiya dubun dubatan mutane na mutuwa a duniya,amma babu wanda ya ce uffan.To me yasa ake ci gaba da gasa wa Saudia aya a hannu?".

Kawo yanzu jakadan kasar Saudia a Comoros,Hamad Ben Muhammad Alhajiri bai ce komai ba game da kalaman nan shugaba Asumani.A cewar jaridar Hürriyet ta kasar Turkiyya,shugaban Hukumar sadarwa ta kasa da kasa ta kasashen da amfani da yaren Faransanci,Asumani yayi faduwar bakar tasa a idon duniya kana ya debo ruwan dafa kansa da kansa.

Haka zalika ya ce: "Muna fatan shugaban Comoros zai lashe wannan aman da yayi.Saboda maganganun da ya furta suka janyo masa bakin jini daga al'umar kasarsa da ma duniya ga baki daya.Tada jijiyoyin wuya da shugabanmu yayi don sukar wata jaridar kasarmu ta yi suka game da kisan wulakancin da aka yi wa dan jarida Jamal Kashoggi abu ne ban tsoro da tayar da hankali.Shin ko mece ce makomar Comoros ?".

Kasar Comoros da ke a gabashin nahiyar Afirka wacce kuma ke da yawan al'uma dubu 800,000 kacal na ci gaba da samun bamban tallafin tattalin arziki daga Masarautar Saudia.

A shekarar bara,Saudia ta bai wa kasar Comoros tallafin da ya haura Dalar Amurka milyan 22,000,000 don samar da ruwan sha da kuma kayayyakin more rayuwa.Labarai masu alaka