Buhari: Boko Haram na samun taimako daga kasashen waje

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, tabbas kungiyar ta’adda ta Boko Haram na samun taimako daga kasashen waje.

Buhari: Boko Haram na samun taimako daga kasashen waje

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, tabbas kungiyar ta’adda ta Boko Haram na samun taimako daga kasashen waje.

A bayanin da Buhari ya yi a Abuja a wajen taron da aka shirya masa shi da mataimakinsa game da shirin zaben da za a gudanar a watan Fabrairu, Buhari ya ce, game da batun yaki da Boko Haram, sojojin Najeriya na bukatar karin makamai da kayan yaki domin samun damar fatattakar ‘yan ta’addar Boko Haram.

Buhari ya kuma ce “Tabbas wasu daga kasashen waje ne suke taimakawa Boko Haram”.

Kungiyar Likitocin Komai da Ruwanka ta bayyana cewa, sakamakon rikicin Boko Haram an kashe dubunnan mutane tare da raba miliyoyi da gidajensu.

 Labarai masu alaka