Wasu masu dauke da makamai sun yi wa bankuna 18 fashi a Itopiya

A jihar Oromiya dake kasar Itopiya wasu mutane dauke da makamai sun aikata fashi a bankuna 18.

Wasu masu dauke da makamai sun yi wa bankuna 18 fashi a Itopiya

A jihar Oromiya dake kasar Itopiya wasu mutane dauke da makamai sun aikata fashi a bankuna 18.

Sanarwar da Ofishin Yada Labarai na jihar ya fitar ta ce, a yankin Wollega an yi fashi a bankuna 18 da suka hada da bankin manoma na Itopiya, Bankin Hadin Kai na Oromiya da Bankin Bayar da Bashi na Oromiya.

Bankunan sun hada da na gwamnati da masu zaman kansu.

Sanarwar ta kuma ce, ‘yan fashin dake dauke da muggan makamai sun yi barna a bankunan na gwamnati da masu zaman kansu inda aka bayyana za a hukunta mutanen kuma ana son jama’a su bayar da hadin kai.

Kafafan yada labaran yankin sun ce, an dora alhakin fashin kan kungiyar ‘Yantar da yankin Oromo.

 Labarai masu alaka