Sudan ta zargi wasu kasasen Yamma da yi mata barazana

Gwamnatin Sudan ta bayyana cewa, sanarwar da kasashen Amurka, Norway, Ingila da Kanada suka fitar game da zanga-zangar da aka gudanar a kasar na dauke da barazana.

Sudan ta zargi wasu kasasen Yamma da yi mata barazana

Gwamnatin Sudan ta bayyana cewa, sanarwar da kasashen Amurka, Norway, Ingila da Kanada suka fitar game da zanga-zangar da aka gudanar a kasar na dauke da barazana.

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Sudan ta fitar ta ce, sanarwar ta kasashe mambobin Trokya da Kanada suka fitar na dauke da barazana kullalliya tare da daukar bangare.

Sanarwar ta ce, a dukkan matakan da Sudan ta dauka ba za ta taba amincewa da katsalandan daga kasashen waje ba, kuma tana da ‘yancin yin abinda take so wanda ya dace da dokokinta.

Sanarwar ta kuma soki Amurka, Nowarwa, Ingila da Kanda bisa yadda suka yi shiru tare da kin la’antar zanga-zangar da aka yi a wata kasa wadda har ma aka kona kayan jama’a da bankuna.

A wata sanarwa da kasashe mambobin Trokya da Kanada suka fitar sun zargi gwamnatin Sudan da amfani da harsashai na gaske wajen harbin masu zanga-zanga wanda hakan abin damuwa ne, kuma duk wani abu da Sudan za ta yi a nan gaba zai iya shafar alakarta da kasashen Trokya da ma sauran kasashen yamma.

A ranar 19 ga watan Disamba ne bayan gwamnatin Sudan ta sanar da kara farashin burudi sai aka fara zanga-zanga a garuruwan Atbera da Port Sudan dake gabar kogin Nil inda daga baya ta zama ta adawa da gwamnati a fadin kasar.

Gwamnati ta sanar da cewar mutane 19 ne suka mutu inda aka jikkata wasu 406 a lamarin.

Mafiya yawan wadanda lamarin ya rutsa da su ‘yan adawa ne.Labarai masu alaka