Kotun Masar ta wanke wasu mambobin Kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi

A Masar kotu ta wanke wasu jagororin kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi su tara wadanda suka hada da Shugaban Majalisar Shura ta Kungiyar Muhammad Badii.

Bayanan da aka samu daga majiyyin Shari’a na cewa, Kotun Hukunta Manyan Laifuka dake Giza ta bayar da hukuncin sallamar Muhammad Badii, mahaifin Shahidiya Asma’u Al-Biltaji mai suna Muhammad Al-Biltaji, Isam Iryan, Basim Avde, Safvet Hijazi da wasu karin mutane 4 da aka zarga da hannu a rikicin masallacin Juma’a na Istikama.

Shugaban lauyoyindake kare mutanen Abdulmumin Abdulmaksud ya yi bayani ga kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa, wannan ne karo na farko da aka ce a sallami Muhammad Badii da wasu jagorin ‘Yan Uwa Musulmi.

Bayan kifar da zababbiyar gwamnatin masar a ranar 3 ga watan Yulin 2013 a ranar 22 ga watan aka samu zanga-zanga a Alkahira Babban Birnin Kasar inda aka kashe mutane 9 tare da jikkata wasu da dama.Labarai masu alaka