Mutane dubu 157,000 da rikicin manoma da makiyaya ya daidaita a Najeriya sun koma gidajensu

Mutane duu dari da hamsin da bakawai (157,000) da rikicin manoma da makiyaya ya raba da matsugunansu sun koma gidajensu a Najeriya.

Kakakin hare-haren Whirl Stroke da aka kaddamar a kasar Manjo Janar Adeyemi Yekini ya ce, a jihohin Benıe, Taraba da Nassarawa an sake tabbatar da tsaro.

Yekini ya ce, a jihohin 3 wadanda suke zaune a tantuna da sansanin 'yan gudun hijira su kimanin dubu dari da hamsin da bakwai sun koma gidajensu saboda samar da tsaro da aka yi. 

Ya ce, tun bayan fara kai hare-haren na Whirl Stroke mutane sama da dubu dari biyu sun koma matsugunansu kuma sun kassara 'yan ta'adda da dama tare da kwace makamai da kayan fada daga gare su.

An kashe daruruwan mutane a Najeriya daga watan Janairu zuwa yau sakamakon rikicin manoma da makiyaya.Labarai masu alaka