Kwalera ta yi sanadiyar rayuka 110 a Najeriya

An bayyana cewar daga farkon shekarar bana kawo yanzu cutar kwalera ta yi sanadiyar mutuwar mutane 110 a Najeriya.

Kwalera ta yi sanadiyar rayuka 110 a Najeriya

An bayyana cewar daga farkon shekarar bana kawo yanzu cutar kwalera ta yi sanadiyar mutuwar mutane 110 a Najeriya.

Hukumar kare yaɗuwar cututtuka a ƙasar ta fitar da sanarwar cewa daga cikin jahohin ƙasar 36 an samu cutar a 29 inda a cikin shekarar bana mutane 110 suka rasu a yayinda dubu 48 da 686 suka kamu da cutar.

Gwamnatin kasar ta tura ma'aikatan lafiya a jahohin Bauchi, Plateau, Zamfara da Adamawa domin kare yaɗuwar cutar.

A yankunan dake fama da matsalar tsaftataccen ruwan sha na yawan fuskantar matsalolin cutar kwalera a Najeriya.Labarai masu alaka