Kungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya ASUU ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani

Kungiyar Malaman Jami'o'i ta Najerıya (ASUU) ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin kasar sakamakon kin aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla da gwamnatin tarayya.

Shugaban Kungiyar Malaman Jami'o'İn Farfesa Biodun Ogunyemi ya sanar da cewa, matakin da suka dauka ya shafi jami'o'in gwamnatin tarayya da na jihohi.

A jawabin da Farfesa Ogunyem, ya yi ga manema labarai bayantaron kwamitin zartarwar kungiya a daren Litinin din nan a Akurre Babban Birnin Jihar Ondo ya ce, yajin aikin ya fara aiki nan take saboda gwamnatin tarayyar Najeriya ta ki girmama duk wata yarjejeniya da suka kulla.

Ya ce, bayan sun yi zaman hakuri da jiran gwamnati ta biya bukatun jami'o'in Najeriya, hakan ya sa su yanke shawarar tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani.Labarai masu alaka