An yi garkuwa da mutane 82 a Kamaru

Kakakin rudunar sojan Kamaru,Kanar Didier Badjeck, ya sanar da cewa,a sayin safiyar jiya,an yi garkuwa da fararen hula 82 a yanki mai amfani da yaren Ingilishi na arewa maso yammacin kasar.

An yi garkuwa da mutane 82 a Kamaru

Kakakin rudunar sojan Kamaru,Kanar Didier Badjeck, ya sanar da cewa,a sayin safiyar jiya,an yi garkuwa da fararen hula 82 a yanki mai amfani da yaren Ingilishi na arewa maso yammacin kasar.

Da yake hira da kafar yada labarai ta Anadolu Agency, Badjeck ya ce,

"Muna kyautata zaton 'yan ta'adda masu akidar aware ne suka yi garkuwa da dalibai 78 da kuma malamai 3 na makarantar Presbyterian Secondary School da ke yankin Bamenda.Kuma tuni jami'an tsaro suka fara kai ruwa rana don ganin an ceto wadanda aka yi garkuwa da su, salim-alim".

Wannan ita ce garkuwa mafi girma da aka taba samu tun a lokacin da rikici ya kunno kai a yanki mai amfani da Ingilishi na Kamaru.

A wata sanarwar da suka fitar a ranar Litinin nan da yamma,'yan aware sun tabbatar da cewa ba su da wata alaka da wannan lamarin,inda suka tuhumi gwamantin Kamaru.

Babban sakataren gwamnatin Ambazonia (Hadakan yankunan masu amfani da yaren Ingilishi na Kamaru),Obadiah Mua ya ce : "Ba sojojin Ambazonia suka sace daliban ba.Muna da masaniya kan bidiyon wannan garkuwar.Ana kokarin shafa mana kashin kaji.Ba zamu taba laminci hakan ba.Muna kira da babbar murya da sojojin Kamaru su gaggauta sakin daliban".

A tun watan Oktoban shekarar 2016,Kamaru ke ci gaba da fama da tashe-tashen hankula a yankunta na arewa maso yammaci da na Kudu maso yammaci,wadanda ke amfani da yaren Ingilishi.

A shekarar 2017,wadannan rikice-rikicen sun yi tsamari sosai inda suka rutsa da rayukan fararen hula da na sojoji da dama tare da tirsasa kusan mutane dubu 40,000 guje wa muhallansu.

 Labarai masu alaka