An kwantar da mutane dubu 10 asibiti sanadiyar wata fitina da ta barke a Afirka ta Tsakiya

An bayyana cewar sanadiyar rikici tsakanin 'yan bindiga a kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya an kwantar da mutane fiye da dubu 10 a asibiti guda.

Likitoci marasa iyaka sun bayyana cewar a yankin Batangafo sanadiyar rikici da ta barke tsakanin yan bindiga a yankin an kwantar da mutane fiye da dubu 10 a asibiti, inda kuma daruruwan mutane suka tsere zuwa gandun daji.

haka kuma sanadiyar rikicin an kone gidaje da dama lamarin da ya sanya anka kafa runfunar mafaka guda uku a yankin. Wasunsu sun rasa rayukansu a yayinda suke jinya a asibitin.

Shugaban likitocin Omar Ahmed Abenza ya bayyana cewar al'ummar yankin na cikin bukatar abinci, tufaffi da makamantarsu.

A kasar an bayyana cewar an cire shugaban majalisar kasar Musulmi Abdul Kerim Meckassou a makon jiya ya fura wutar rikin kasar.

A kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya 'yan bindiga kungiyar Seleka sunka fara kalubalantar gwamnati a shekarar 2012, a yayinda wasu kungiyar Kiristawa Anti-Balaka da Seleka suka dinga haddasa rikicin da ya yi sanadiyar rayukan musulmin kasar da dama. Duk da zaben shugaban kasar da aka gudanar a 2016 har ila yau kasar na fuskantar rigingimu yau da kullun. Labarai masu alaka