Amurka ta sake kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 60 a Somaliya

Sansanin Sojin Amurka da ke Afirka (AFRICOM) ya sanar da kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 60 a wasu hare-hare da suka kai a Somaliya.

Amurka ta sake kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 60 a Somaliya

Sansanin Sojin Amurka da ke Afirka (AFRICOM) ya sanar da kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 60 a wasu hare-hare da suka kai a Somaliya.

Sanarwar da aka fitar daga AFRICOM na cewa, dakarun Amurka tare da na Tarayyar Somaliya a ranar 12 ga watan Oktoba sun kai hare-hare a kusa da kwarin Harar tare da kashe 'yan ta'addar Al-Shabab.

Sanarwar ta ce, ba a sami farar hula ko daya ba a harin.

An bayyana cewa sakamakon harin an kashe 'yan ta'addar na Al-Shabab sun kai su 60. A wani harin da aka kai a sansanin Al-Shabab a ranar 21 ga watan Nuwamban 2017 an kashe mambobin 'yan ta'addar kusan 100.Labarai masu alaka