Ebola ta kashe mutane 83 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

Mutanen da annobar cutar Ebola suka kashe a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo sun kai tamanin da uku (83).

Ebola ta kashe mutane 83 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

Mutanen da annobar cutar Ebola suka kashe a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo sun kai tamanin da uku (83).

Sanarwar da Ma'aikatar Lafiya ta Jamhuriyar Demokradiyar Kongo ta fitar ta ce, tun daga watan Yuli zuwa yau mutane dari da tamanin da takwas ne (188) ne suka kamu da wata cuta ta zubar da jini a arewacin Kivu.

Daga cikin wadannan mutane dari da hamsin uku (153) na dauke da cutar Ebola.

Sakamakon yadda wasu biyar suka sake mtuwa daga cikin 153 ya sanya adadin wadanda cutar ta kashe sun kai 83.

Adadin wadanda suka warke bayan kamuwa da cutar kuma sun kai mutane 51.

Haka zalika daga cikin mutane 188 akwai 35 da suka mutu wadanda ba a tabbatar ko Ebola ce ta kashe su ba.

Sakamakon yadda ba a samu damar gwajin me ya kashe su ba a tabbatar da sababin ajalinsu ba.

A gefe guda kuma an yi wa mutane dubu 15 allurar riga kafi a wani bangare na gangamin da aka fara a watan Agusta.

Da fari a shekarar 1976 ne cutar Ebola ta bulla a kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

A tsakanin shekarun 2014-2017 cutar ta kama mutane sama da dubu 30 yayinda sama da dubu 11 suka mutu a kasashen Saliyo, Gini da Laberiya da ke Yammacin Afirka.


Tag: Kongo , Mutu , Ajali , Ebola

Labarai masu alaka