Mutane da dama sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Kano da ke Najeriya

Mutane 19 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Mutane da dama sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Kano da ke Najeriya

Mutane 19 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Jami'in Hukumar Bayar da Agajin gaggawa ta (SERERA) da ke Kano Alhaji Bashir Ali ya bayyana cewar a yankunan Rimin gado, Gabasawa da Getso na jihar an samu mamakon ruwan sama tsawon kwanaki 2 wanda hakan ya janyo ambaliya.

Bashir ya ce, mutane 19 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar.

Bashir ya kara da cewar, ambaliyar ta janyo rushewar gidaje 70 inda kadada da dama na gonaki ya samu matsala.

Ya ce, an aike da jami'an bayar da agaji zuwa yankunan kuma ana fargabar za a iya samun karin mutanen da za su mutu.

Ana ci gaba da samun ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama da ake ci gaba da samu a arewacin Najeriya.

A watanni 2 da suka gabata mutane akalla 70 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Najeriya.Labarai masu alaka