Karyewar gada ya janyo tireloli 732 kasa shiga Nijar daga Benin

Motocin tirela 732 ne suka makale a Jamhuriyar Benin tare da gaza shiga Jamhuriyar Nijar saboda karyewar wata gada da ta hada kasashen 2.

Labaran da kafafan yada labaran yankin suka fitar na cewa, a makon da ya gabata ne bayan samun mamakon ruwan sama gadar kogin Nijar ta samu matsala.

Sakamakon wannan matsala ya sanya tireloli 732 kasa shiga Nijar inda suka tsaya a Benin.

Sakatare Janar na Kungiyar Masu Fitar da Kaya zuwa Nijar Chaibou Tchombiano ya sanar da 'yan jaridu cewar motocin tirelar har guda 732 sun tsaya a Benin tare da kasa shiga Nijar saboda karyewar gadar.

Ya ce, wadannan tireloli na dauke da kayan abinci, magunguna, da sauransu wadanda a nan gaba dan ba a samar da su a Nijar ba za a samu matsala.

Tchombiano ya bayar da shawara ga mahukuntan Benin da su yi amfani da hanyoyin Najeriya wajen kai kayan Nijar kafin a samar da sabuwar gada.

Nijar na daya daga cikin kasashen duniya da suke fama da yunwa.

Tag: Gada , Benin , Nijar , Tirela

Labarai masu alaka