An raba mutane dubu 50 da matsugunansu a Mali

A rikicin da aka yi a tsakanin jami'an tsaro da dakarunsu da aka yi a Mali a wannan shekarar ta 2018 an raba mutane sama da dubu 50 da matsugunansu.

An raba mutane dubu 50 da matsugunansu a Mali

A rikicin da aka yi a tsakanin jami'an tsaro da dakarunsu da aka yi a Mali a wannan shekarar ta 2018 an raba mutane sama da dubu 50 da matsugunansu.

Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa, a kasar ta Mali da ke da mutane kusan miliyan 20 matsalar tsaro ta janyo arangama da dama.

Duk da sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati ta yi da 'yan aware na arewacin Mali a kasashen Chadi da Aljeri a kokarin neman an zauna lafiya, amma ana ci gaba da fafata rikici.

A Bamako Babban Birnin Kasar Mali, Kidal, Menaka, Gao, Timbuyktu, Taodenit, Mopti da Segou an samu arangama da dama tsakanin jami'an tsaro da 'yan tawaye inda aka raba mutane sama da dubu 50 da gidajensu.

Tag: Arangama , Hari , AQIM , Mali

Labarai masu alaka