Adadin mutanen da Ebola ta kashe a Kongo ya karu

Ya zuwa yanzu mutane 59 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Adadin mutanen da Ebola ta kashe a Kongo ya karu

Ya zuwa yanzu mutane 59 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo. 

Ma'aikatar Lafiya ta Kasar ta bayyana cewa, a karshen watan Yuli ne cutar ta sake bulla a jihar Arewacin Kivu inda aka samu mutane 131 suna zubar da jini wanda bayan bincike aka gano 100 daga cikinsu na duke da cutar Ebola.

Sakamakon mutuwar karin mutane 5 daga cikin 100 ya sanya adadin wadanda suka mutu ya kai mutum 59.

Akwai kuma mutane 30 daga cikin 131 da suka mutu amma ba a gano suna dauke da Ebola ba.

Saboda yadda ba a iya yin gwaji ga mutanen da suka mutun ba shi ya sa ba a tabbatar da me ya kashe su ba.

A karkashin gangamin da aka fara a yankin a watan Agusta an yi wa mutane sama da dubu 7 allurar riga-kafi.

A wancan karon an gano bullar Ebola a jihar Ekwador.

A shekarar 1976 ne cutar Ebola ta bulla a Kongo inda a 2013 ta yadu a Yammacin Afirka.

Mutane sama da dubu 11 cutar ta kashe a tsakanin 2014-2017 a kasashen Gini, Laberiya da Saliyo da ke Yammacin Afirka.Labarai masu alaka