Aljeriya za ta fara samar da maganin kansa

Kasar Aljeriya ta yanke shawarar zuba zunzurutun kudi Yuro milyan 20 don fara samar da maganin da zai warke cutar daji kwata-kwata.

Aljeriya za ta fara samar da maganin kansa

Kasar Aljeriya ta yanke shawarar zuba zunzurutun kudi Yuro milyan 20 don fara samar da maganin da zai warke cutar daji kwata-kwata.

Jaridar kasar Aljeriya, L'Expression ce ta bayar da wannan albishirin,inda ta kara da cewa,

"Nan da wani matsakaicin zamani,kamfanin samar da magunguna na Faransa IPSEN wanda ya kwashe shekaru 10 a Aljeriya ya sanar da cewa zai bude wani sabon kamfani mai suna Ipsen Pharma-Aljeriya a karshen shekarar bana.Tuni Aljeriya da IPSEN suka kammala gwaje-gwaje da kuma duk wani binciken da ya kamata a ce a gudanar.Abu daya tilo da ya rage a yanzu, shi ne fara samar da maganin.Za a soma amfani da maganin kansar a Aljeriya kafin a  siyar da shi a duk fadin duniya".

 Labarai masu alaka