Motsawar kasa ta afku a wasu sassan Abuja Babban Birnin Najeriya

Al'umar yankin Mpape da ke Abuja Babban Birnin Najeriya sun girgiza matuka game da motsawar kasar da ta afku a yankinsu.

Motsawar kasa ta afku a wasu sassan Abuja Babban Birnin Najeriya

Al'umar yankin Mpape da ke Abuja Babban Birnin Najeriya sun girgiza matuka game da motsawar kasar da ta afku a yankinsu.

Rahotanni sun ce, a tun ranar Larabar da ta gabata ake samun motsin kasa wanda ya firgita jama'ar birnin na Abuja.

Mpape yanki ne da ya ke da kamfanunnukan fasa duwatsu kuma yana da tsaunuka da yawa a cikinsa.

Mazauna yankin sun ce, da farin sun dauyka lamarin na afkuwa ne sakamakon fasa duwatsun da ake yi, amma daga baya sai suka ga ya wuce ka'ida.

An bayyana cewar wasu gidaje da hanyoyi sun samu matsala a yankunan.

Ba kasafai abu irin wanna ya ke afkuwa a Najeriya ba.

Hukumar Kula da Yanayin Kasa ta Najeriya ta sanar da aika jami'anta zuwa wajen da lamarin ya afku.Labarai masu alaka