Mummunar ambaliyar ruwa a jihar Naija

Wata mummunar ambaliyar ruwa da ta afka wa Jihar Naijan Tarayyar Najeriya, ta yi sanadiyar rayukan mutane 14.

Mummunar ambaliyar ruwa a jihar Naija

Wata mummunar ambaliyar ruwa da ta afka wa Jihar Naijan Tarayyar Najeriya, ta yi sanadiyar rayukan mutane 14.

Shugaban Hukumar agajin gaggawa na wannan yankin da ke tsakiyar Najeriya,Elhaji Garba Salisu ya ce,sabili da irin barnar da ruwa ya yi a sassan daban-daban na Naija, an samu mutane 14 da suka riga mu gidan gaskiya.

Salisu ya kara da cewa, tuni suka fara kai wa wadanda lamarin ya tsunduma halin kaka-ni-kayi, dauki.Haka zalika suna ci gaba da waye jama'a kai kan su guji gina muhallansu a hanyoyin ruwa ke bi.

Garba Salisu ya ce,"Ambaliyar ruwa ta haifar da zaizaiyar kasa a Naija.Abinda na ke tsoro shi ne, kar ta yi awon gaba da mutane a tsakiyar dare yayin da suke barci.Shi yasa bai kamata ba mu toshe hanyoyin da aka kebe don ruwa".

A Najeriya damana na sauya fuska daga wannan jihar ya zuwa wancan,amma inda aka dubi kasar ga baki dayanta, kusan watannin shida ake yi ana sheka ruwa, watanni shida kuma ana rani.Labarai masu alaka