Sojojin Kenya 5 sun mutu a iyakar kasar da Somaliya

Sojojin Kenya biyar ne suka rasa rayukansu a lokacin da motar da suke ciki ta taka wani bam da aka binne a kasa a kan iyakar kasar da Somaliya.

Sojojin Kenya 5 sun mutu a iyakar kasar da Somaliya

Sojojin Kenya biyar ne suka rasa rayukansu a lokacin da motar da suke ciki ta taka wani bam da aka binne a kasa a kan iyakar kasar da Somaliya.

Kakakin Rundunar Sojin Kenya Pauş Njuguna ya ce, an kai wa sojojin hari a lokacin da suke aiyukan jin kai wajen deboruwa tare da kai wa jama’ar garin Lamu.

Rahotanni sunm ce, lamarin ya afku a kan hanyar Kiunga da Sankuri.

Kakakin Sojin ya kara da cewa, wasu karin sojoji 10 sun samu raunuka.

Yankin dai na fama da ‘yan ta’addar Al-Shabab saboda kusancin da yake da shi Somaliya wadda nan ce matattararsu.

Harin ya zo ne a lokacin da Shugaban Kasar Kenya uhuru Kenyatta ya koma gida bayan ya ziyarci Amurka inda suka kulla yarjejeniyar yaki da ta’addanci da Donald Trump.

 Labarai masu alaka