Tsananin ruwan sama ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi a Nijar

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ruwan ƙanƙara masu ɗinbin yawa sun yi sanadiyar salwantar rayuka 22 a ƙasar Nijer.

Tsananin ruwan sama ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi a Nijar

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ruwan ƙanƙara masu ɗinbin yawa sun yi sanadiyar salwantar rayuka 22 a ƙasar Nijar.

Ministan bayar da agajin gaggawa Laouan Magadji ya yi sharhi a gidan talabijin ƙasar inda ya bayyana cewar tsananin ruwan ya faru tsakanin 1 ga watan Yuli zuwa 6 ga watan Agusta.

Magadji, ya bayyana cewar a cikin wannan lokaci tsananin ruwan sama da kwararowar ruwa sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 22, rushewar gidaje dubu 3 da 131 da kuma ɓarnata gonai masu yawan hekta dubu 3 da 902.

Lamarin dai ya shafi mutane dubu 49 da 845, a inda mutane dubu 2 suka rasa gidajensu a babban birnin kasar.

A shekarar bara ma ruwan sama da ya haifar da gudanar ruwa ya janyo mutuwar mutane 56 inda fiye da mutane dubu 206 suka kasance cikin halin ƙaƙanikayi.

 Labarai masu alaka