Dubun wasu 'ƴan ta'addar Boko Haram ta cika

Rundunar sojan Najeriya ta kashe wasu mambobin ƙungiyar ta'adda ta Boko Haram 7 a wani farmaki da ta kai a yankunan Borno dake arewa maso gabashin ƙasar.

Dubun wasu 'ƴan ta'addar Boko Haram ta cika

Rundunar sojan Najeriya ta kashe wasu mambobin ƙungiyar ta'adda ta Boko Haram 7 a wani farmaki da ta kai a yankunan Borno dake arewa maso gabashin ƙasar.

Mai magana da yawun "Operation Lafiya Dole" Onyema Nwachuku ya shaidawa manema labarai da cewa rundunar ta fattataki ƴan ta'addar Boko Haram a yankin Guzamala dake jihar Borno a Najeriya.

Baya ga waɗanda aka kashe, an raunana ƴan ta'adda da dama.

A ɗayan barayin kuma, an bayyana cewar a wani hari da aka kai sansanin sojoji a kauyen Garunda da yawan jami'an tsaro sun rasa rayukansu.

Boko Haram da ta ɓullo a shekarar 2000 ta soma ƙaddamar da hare-haren ta'addanci a shekarar 2009 a yayinda kawo yanzu ta yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dubu ashirin.

Haka kuma daga shekarar 2015 ta fara ƙaddamar da hare-haren ta'addanci a ƙasashen da suke makwabtaka da Najeriya da suka haɗa da Kamaru, Benin, Chadi da Nijer.

Ƙungiyar ta hallaka fiye da mutane dubu biyu a yankin tafkin Chadi.

 Labarai masu alaka