An kashe sojojin Kenya 5 a wani hari da 'Yan ta'adda suka kai musu

Sojojin Kenya 5 ne suka mutu yayinda wasu da dama suka jikkata a ranar Larabar nan bayan da 'yan ta'addar Al-Shabab suka tayar da wani bam da suka binne a lokacin da sojojin ke sintiri a gabar tekun kudancin kasar.

Wani jami'in dan sanda a garin Lamu da ke gabar teku ya shaida cewa, a harin da aka kai an jikkata wasu 'yan sanda 2 da suke cikin mummunan hali.

Shaidun gani da ido sun shaida wa gidan Talabijin na Kenya cewa, jami'an soja ne suka taka wani bam a aka binne  kan hanya a yankin na Lamu inda aka kai 6 daga cikinsu zuwa asibiti.

Dajin Boni da ke Kenya ya zama matattarar 'yan ta'addar Al-Shabab da suke da helkwatarsu a Somaliya. 

'Yan ta'addar na haura wa zuwa Kenya tare da kai wa jami'an tsaro hari.

Kenya ta fara kai wa 'yan ta'addar hare-hare a shekarar da ta gabata.Labarai masu alaka