An kama wani sojan Amurka da ya aikata damfara a Najeriya

Jami'an 'yan sanda na musamman sun kama wani sojan Amurka a kudancin Najeriya bayan da ya damfari wasu mata 3 ta yanar gizo kan zai sama mata Visa.

An kama wani sojan Amurka da ya aikata damfara a Najeriya

Jami'an 'yan sanda na musamman sun kama wani sojan Amurka a kudancin Najeriya bayan da ya damfari wata mace ta yanar gizo kan zai sama mata Visa.

'Yan sandan masu yaki da aikata manyan laifuka sun kama Garrick Michael Ba'amurke bayan da ya zambaci mata 3 kan zai sama musu Visa zuwa kasarsa.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya yarawaito Kwamishinan 'yan sandan jihar Imo Dasuki Galadanchi na cewa, mutanen da Michael ya zambata sun hada da Sylva Chineyenwa, Wuchi Peace, da Duny Glory.

Michael ya kuma bayyana damfarar mata da yawa bayan ya yi musu alkawarin samo Visar zuwa Amurka.

Ba'amurka ya ce, ya zo Najeriya ne don ziyartar matarsa da ke rayuwa a kasar inda a nan ne ya hadu da mutanen da ya damfara.

AALabarai masu alaka