Cutar amai da gudawa ta kashe mutane 19 a Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa, mutane 19 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Kwalara a Kasar.

Cutar amai da gudawa ta kashe mutane 19 a Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa, mutane 19 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Kwalara a Kasar.

Mahukunta sun ce, an kai mutane 65 asibiti sakamakon bullar cutar a jihar Niger.

Mahukuntan yankin sun ce, jama'a sun dimauce sakamakon bullar annobar inda aka shawarci mutane da sun ga alamun ta a jikinsu su je asibiti mafi kusa.

Yadda ba a samun kyakkyawan ruwan sha a Najeriya, tare da yadda ba a iya maganin annoba a lokacn da ya kamata da karancin kayan aiki na janyo hatsarin rasa rayuka.

Akwai cututtuka irin su zazzabin cizon sauro, typhoid, shanyewar jikin yara kana, amai da gudawa da kyandar biri dake damun jama'ar Najeriya.Labarai masu alaka