Turkiyya ta tallafa wa iyalai marasa galihu dubu 300,000 a Kano da Kaduna

A tsawon watan Ramadan,kungiyoyin bada agaji na Turkiyya sun shirya walimomin buda-baki da dama,gina rijiyoyi da kuma tallafa wa sama da iyalai marasa galihu dubu 300,000 a sassa daban-daban na Najeriya.

Hukumar Kula da Al'amuran Addinai ta Turkiyya Diyanet (TDV) da sauran kungiyoyin agaji sun raba wa marayu da mata tufafi,gina rijiyoyi da kuma shirya walimomin buda-baki a tsawon wata mai alfarma.

RDV ta tallafa wa daruruwan iyalan Najeriya a albarkacin wani shiri mai taken "Kar ka manta 'yan uwanka,suna jira".

Ali Kashikirik, shugaban reshen TDV da ke Abuja ya sanar wa kafar yada labarai ta Anadolu Agency cewa,

"A tsawon watan Ramadan,mun share kwallan marasa galihun Legas da kuma raba kayan masarufi a sansanonin masu neman mafaka na Abuja.Haka zalika mun gana da marasa gatan da ke kauyukan Najeriya.Kusan 'yan Najeriya 3000 na birane daban-daban aka bai wa taimako".

Kungiyar bada agaji ta wasu Turkawa da ke kasashen ketare,sun taimaka wa kusan iyalai 300,000 a yankunan Kaduna da Kano.

Kungiyar bada agaji ta Abuja-Istanbul Friendship Association ta tallafa wa iyalai marasa galihu 2000 da kuma raba wa yara mata 500 tufafi

Baya ga haka ta bada tallafin cimaka ga iyalai 1800 a tsawon watan Ramadan, da gayyatar 'yan Najeriya dubu 20,000 a walimomin buda baki tare da raba wa iyalai 2000 nama".

 Labarai masu alaka