Kotu ta hana tsohon gwamnan Kano Shekarau tafiya Umrah

Kotun Gwamnatin Tarayya da ke jihar Kanon arewacin Najeriya ta hana tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau tafi ya Umrah a kasar Saudiyya inda ta ki ba shi fasfonsa.

Kotu ta hana tsohon gwamnan Kano Shekarau tafiya Umrah

Kotun Gwamnatin Tarayya da ke jihar Kanon arewacin Najeriya ta hana tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau tafi ya Umrah a kasar Saudiyya inda ta ki ba shi fasfonsa.

Malam Shekarau ya tunkari kotun tare da neman ta bayar da umarni ga mataimakin rejistara ya ba shi fasfonsa na tafiya don ya samu damar zuwa Umrah a tsakanin 30 ga watan Mayu zuwa 23 ga watan Yuni.

Jaridar yanar gizo ta Daily Nigerian ta rawaito cewa, Alkaliyar kotun Mai Shari'a Zainab Abubakar ta ki amince wa da bukatar ta Shekarau inda lauyan gwamnati Johnson Ojogbane ya mika wani bayani na hujjoji mai yawan sakin layi tare inda ya nuna rashin amincewa da bukatar tsohon gwamnan.

A zaman Shari'ar da aka yi a ranar Talatar nan lauyan Shekarau Abdul Adamu ya mika wa kotun tasu bukatar.

Bayan haka ne lauya Ojogbane ya mika nasa bayanin mai sakin layi 9 tare da kira ga kotun da kar ta bayar da dama ga Shekarau ya tafi Umrah.

Mai Shari'ar ta yanke hukunci da cewa, duba da yadda fasfon mutumin da ake tuhuma ya kasance daya daga cikin sharuddan bayar da belinsa, bayan shawara ta yanke hukuncin kin bayar da umarnin sakin fasfon nasa.

An gurfanar da Shekarau tare da Aminu Wali da Mansur Ahmad a gaban kotu bisa zarginsu da karbar Naira miliyan 950 wanda wani bangare ne na dala miliyan 115 da aka zargi tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya Diezani Alison Maduekwa da raba wa a lokacin da zaben 2015 ya karato.Labarai masu alaka