Buhari: 'yan Najeriya ba zasu taba yarda da rashin adalci ba

Shugaban Taryyar Najeriya,Muhammadu Buhari ya ayyana 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin ranar karrama gwarzayen demokradiyya,wadanda a ciki har da Moshood Abiola,wanda ya kwanta dama a kurkuku.

An bada lambar karrmawa ta "Grand Commander of the Federal Republic" daya daga cikin manyan lambobin masu kima da aka kebe wa shugabannin kasa,ga marigayi Abiola wanda ya rasu a gidan kwafi a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1998 da lambar "Grand Commander of the Order of Niger (GCON) ",lamba ta 2 mafi girma ga Babagana Kingibe.

Haka zalika an bai wa mai fafutukar kare hakkin bil adama Gani Fawehinmi, wanda ya share shekaru da dama sansanin azabtarwa na sojojin Najeriya,lambar ta GCON.

Yayin wani jawabi da yayi gaban iyalan gwarzayen ranar 12 ga watan Yuni da manya-manyan jiga-jigan gwamnati, Shugaba Buhari ya ce,

"Bamu dauki matakin karrama gwarzayen ranar 12 ga watan Yuni, da nufin tuna munanan ababen da suka afku a baya ba, mun yi hakan ne don haskaka alkiblar al'umarmu.Gwamnatin Ibrahin Babangida ya soke sakamkon zaben ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993,duk da cewa an san wanda ya ci zabe.Ba zamu iya dawo baya ba,amma muna iya akalla tausasa zukatanmu.'Yan kasar Najeriya ba za taba yarda da rashin adalci ba.manufarmu ita ce martaba ranar 12 ga watan Yunin don amfanin kasarmu".Labarai masu alaka