Yara 25 sun mutu a Najeriya saboda matsalar Cimaka

A cikin watanni 4 da suka gabata yara kanana 25 ne suka mutu inda ake kula da lafiyar wasu dubu 19 sakamakon matsalar Cimaka a jihar Jigawa ta Najeriya.

Daraktan Sashen Kula da Cimaka na Jihar Saidu Umar ya fitar da rubutacciyar sanarwa cewa, a watanni 4 yara 25 sun mutu saboda matsalar cimaka.

Umar ya ce, a tsakanin watan Janairun da Afrilun 2018 yara kanana dubu 18,652 aka kai asibiti saboda matsalar cimaka kuma akalla 25 daga cikinsu sun mutu.

Sanarwar ta Umar ta kara da cewa, a shekarar 2017 Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da taimakon abinci ga yara kanana dubu 10 a jihar ta Jigawa.Labarai masu alaka