Gwamnatin Najeriya na ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa ba kakkautawa

Kotu a Najeriya ta aike da tsohon gwamnan jihar Plateau kuma Sanata Jonah-Jang zuwa gidan maza sakamakon tuhumarsa da laifukan cin hanci da Rashawa na dalar Amurka miliyan 17.5.

Hukumar yaki da Cin hanci, Rashawa da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zakon Kasa ta Najeriya (EFCC) ta fitar da wata rubutacciyar sanarwa inda ta ce, an gurfanar da Jang a gaban kotu saboda tuhumar da ake yi masa.

A zaman Shari'ar Babbar Kotun Legas ta yi Sanata Jang ya musanta zarge-zargen da ake yi masa, kotun ta dage zaman shari'ar zuwa 24 ga watan June inda ta bayar da umarnin da a kai Jang gidan kurkuku.

A lokacin da Jang ya mulki jihar an zarge shi sace dala miliyan 17.5 da Babban Bankin Najeriya ya ba wa jihar don tallafawa masu kanana da matsakaitan sana'o'i.

Rahotanni sun ce, a lokacin mulkin Jang ne 'yan ta'addar Boko Haram suka fara kai hari a jihar Plateau da ke Tsakiyar Najeriya.Labarai masu alaka