Tarayyar Afirka ta bukaci a shawo kan rikicin Siriya

Tarayyar Afirka ta bukaci a yi amfani da hanyoyi na siyasa wajen kawo karshen rikicin Siriya da ya dauki tsawon shekaru 7.

Tarayyar Afirka ta bukaci a shawo kan rikicin Siriya

Tarayyar Afirka ta bukaci a yi amfani da hanyoyi na siyasa wajen kawo karshen rikicin Siriya da ya dauki tsawon shekaru 7.

A wata sanarwa da Tarayyar ta fitar ta soki hari da makamai masu guba da aka kai a Gabashin Guta da ke Siriya tare da kashe fararen hula 78 inda aka jikkata daruruwa.

Sanarwar ta ce, Tarayyar Afirka na goyon bayan demokradiyya a kasashen duniya kuma duk wani abu da za a yi wata kasa dole ya zama bisa dokokin kasa da kasa.

Tarayyar ta kuma ce, tana suka da babbar murya kan yadda alka yi amfani da makamin da dokokin kasa da kasa suka haramta amfani da shi.Labarai masu alaka