Mutane 5 sun mutu a wani hari da aka kai a filin wasan kwallo a Somaliya

Mutane 5 ne suka mutu yayin wasu 10 suka jikkata sakamakon harin bam da aka kai a wani filin wasan kwallon kafa da ke garin barawe na yankin lower Shabelle a Somaliya.

Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sandan yankin Shabelle Bashir Mohamed Yusuf ya shaida wa manema labarai cewa, an nufi masu buga kwallo da masu kallo a harin bam din inda aka tabbatar da jikkatar wasu mutane 10 baya ga 5 da suka mutu.

Ya ce, an kai wadanda suka jikkata zuwa sibiti.

An kai harin a lokacin da kungiyoyin Elman da SYL suke buga wasa.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin amma an dora shi kan kungiyar ta’adda ta Al-Shabab.Labarai masu alaka