• Bidiyo

Turkiyya ta jajanta wa daukacin al'umar Najeriya

Kasar Turkiyya ta la'anci tagwayen hare-haren kunar bakin waken da aka kai a jihar Borno da ke a Arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya, a ranar Asabar din nan ta ta gabata.

Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya, ya la'anci hare-haren ta'addancin da aka kai a kasuwar garin Konduga na Borno.

Akalla mutane 21 ne sun mutu,inda wasu 22 kuma jikkata sakamakon wannan ta'asar da ta afku.

Turkiyya ta jaddada goyon bayanta ga Najeriya tare da mika gaisuwar ta'aziyyarta ga iyalan wadanda suka kwanta dama da kuma jinya, shugabanni da daukacin al'umar Najeriya wacce ke ci gaba da fama da hare-haren ta'addanci da na ha'inci.

 Labarai masu alaka