Albishir daga shugaba Buhari zuwa 'yan Najeriya

A wannan makon,shugaban Tarayyar Najeriya,Muhammadu Buhari yayi wa daukacin al'umarsa babban albishir da nufin faranta zuciyoyinsu

Albishir daga shugaba Buhari zuwa 'yan Najeriya

A wannan makon,shugaban Tarayyar Najeriya,Muhammadu Buhari yayi wa daukacin al'umarsa babban albishir da nufin faranta zuciyoyinsu.

A 'yan shekarun da suka gabata, cin hanci da rashawa, almundaha, sama da fadi da kuma babakere da dukiyar al'uma ta zama ruwan dare gama duniya a illahirin kusurwowin Najeriya,abinda ya durkusar da tattalin arzikinta tare da yi wa rayuwar jama'a daurin gwarmai.

A shekarar 2019,hawansa kan karagar mulki ke da wuya,shugaba Buhari ya daura damarar kawo karshen wadannan manyan matsalolin da suka kassara cigaban kasarsa.

A wannan makon, Buhari ya zo da babban albishir ga al'umarsa,inda yayi alkwarin siyar da dukannin kadarori da hannayen jarin da ya kwato daga hannun wadanda suka aikata halin bera don zuba kudaden a baitulmalin Najeriya,da zummar share kwallan talakawansa.

 

 Labarai masu alaka