Sabon shugaban kasar Afirka ta Kudu ya zo da "Farar Aniya"

Sabon shugaban kasar Afrika ta Kudu Matamela Cryil Ramaphosa a yayinda yake jawabinsa ta farko ga al'ummar kasar ya yi alkawarin yakar cin hanci da rashawa da kuma sake farfado da tattalin arzikin kasar.

Ramaphosa, ya bayyana a gaban majalisar kolin kasar a inda ya tabbatar da aniyarsa na fatattakar cin hanci da rashawa daga ma'aikatun kasar baki daya. Bugu da kari, ya kuma daura damarar samar da aikin yi  da kuma bunkasa fanunkan yawon bude ido, noma, kyere-kyere da hakkar ma'adanai.

Ya bayyana farar aniyarsa na kafa kungiyar samar da aikin yi ga matasa ta horar da matasa miliyan daya a fannuka daban-daban cikin shekaru uku.

Jam'iyyar African National Congress watau ANC ta nada shugabanta a matsayin shugaban kasa bayan tsohon shugaba Jacob Zuma ya yi murabus.

 Labarai masu alaka