An kashe sojoji 3 a yayin rikici da 'yan awaren Kamaru

Sojoji 3 ne suka mutu sakamakon rikicin da suka yi da 'yan awaren yakin yammacin Kamaru da ke magana da yaren Ingilishi.

An kashe sojoji 3 a yayin rikici da 'yan awaren Kamaru

Sojoji 3 ne suka mutu sakamakon rikicin da suka yi da 'yan awaren yakin yammacin Kamaru da ke magana da yaren Ingilishi.

Kakakin Rundunar Sojin Kamaru Kanal Didier Badjeck ya ce, duk da sanar da dokar hana fita a yankin a ranar Asabar din da ta gabata amma sai daka samu arangama inda sojoji 3 suka mutu.

Badjeck ya kuma kara da cewa, 'yan awaren sun yi garkuwa da mataimakin shugaban karamar hukumar yankin.

A watanni 3 da suka gabata sojojin Kamaru 25 ne suka mutu inda dubunnan fararen hula dubu 33 suka gudu Najeriya sakamakon arangamar da suka yi da 'yan aware a yammcin kasar.Labarai masu alaka