Matan Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo 510 aka yi wa fyade a 2017

Wata Kungiyar Kare Hakkokin Yara Kanana da Dalibai LIZADEEL ta bayyana cewa, a shekarar 2017 da ta gabata an yi wa mata 510 fyade a Kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Shugaban Kungiyar a Kasar Jean-Malhys Lungala ya sanar da cewa, 405 daga cikin matan yara ne kanana inda aka kuma tura 500 zuwa asibitoci don auna lafiyarsu.

Lungala ya ce, ;yan tawayen Kamuina Nsapu ne suka aikata kaso 80 cikin 100 na fyaden da aka yi wa matan.

Ya kara da cewa, Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF na taimaka wadanda aka yi wa fyade a kasar ta hanyar samar musu da abubuwan da suke hana kamu wa da cutar Kanjamau.

Rahoton da aka fitar ya ce, mutane 350 sun shigar da kara kotu game da fydaen da aka yi musu.Labarai masu alaka