Yara kanana 5 sun mutu sakamakon fashewar Gurneti a Tanzaniya

Yara 'yan makaranta 5 ne suka mutu inda wasu 42 suka samu raunuka sakamakon fashewar da Gurneti ya yi a makarantar Firamare ta Kihinga da ke Ngara a yankin Kagewa na arewa maso-yammacin kasar Tanzaniya.

Shugaban 'Yan sandan yankin Augustine Ollomi ya tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na Anadolu inda ya ce, an kai harin a lokacin da daliban ke tafiya azuzuwansu.

Ollomi ya kara da cewa, yara 3 sun mutu nan take yayinda 2 suka rasu bayan an kai su asibitin Rulenge.

Ya ce, binciken farko da aka gudanar ya ce, wani dalibi ne ya tsinci Gurneti akan hanyarsa ta zuwa makaranta kuma ya saka shi a jakarsa wanda sakamakon fashewarsa ne aka samu asarar rayuka da jikkatar wasu.

Ya kara da cewa, yaran da suka mutu na da shekaru 8 zuwa 13.Labarai masu alaka